Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana rashin jin dadinta bisa samun rahotanni kan yadda wasu shugabannin majalisun kananan hukumomin jihar nan masu barin gado ke yanka gandun daji da gonaki da kuma filayen gwamnati suna sayarwa daidaikun jama’a a yankunan su.

Wata sanarwa mai dauke daga kwamishinan ma’aikatar kasa da samar da gidaje da raya birane da tsara yankunan na jihar Jigawa Hon. Sagiru Musa Ahmad ta ce gwamnati ta soke dukkan takardun mallakar irin wadannan filaye da gonaki da shugabannin majalisun kananan hukumomin suke sayarwa jama’a.

Sanarwar ta shawarci duk wanda ya sayi irin wadannan filaye daga shugabannin kananan hukumomin da ya je wurin wanda ya sayar masa domin karbar kudinsa domin gwamnati ba za ta lamunci sayar da filayen ba bisa ka’ida ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: