Kusan mako guda bayan dakatar da shafin Twitter, gwamnatin tarayya ta shiga Koo, wani dandalin sadarwa na kasar Indiya.

A makon da ya gabata, kamfanin na Twitter ya janye sakon da Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta a kan yakin basasa.

Kwana uku bayan haka, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Twitter, tana mai cewa yana kafar ungulu ga bukatun kasar.

‘Yan Najeriya sun tsallake haramcin amfani da Twitter ta hanyar amfani da VPN, amma Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar gurfanar da wadanda suka karya dokar haramcin.

Hukumar Watsa Labarai ta Kasa ta kuma umarci gidajen talabijin da na rediyo da su fita daga Twitter.

Akwai korafe-korafe game da rashin yada labarai sakamakon haramta Twitter.

Watakila a matsayin samo mafita bayan haramcin, gwamnatin tarayya ta shiga sabon dandalin na Koo.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: