Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yaki da rashawa a tsarin mulkin siyasa na da wuyar sha’ani.

0 66

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yaki da rashawa a tsarin mulkin siyasa na da wuyar sha’ani sosai.

Shugaban kasar ya sanar da haka a yau yayin da aka yi fira da shi a gidan talabijin na Arise TV.

A cewarsa, yaki da rashawa ya wahalar da shi tun bayan da ya zama zababben shugaban kasa na mulkin demokradiyya shekaru 6 baya.

Sai dai, ya nanata cewa gwamnatinsa ta samu nasarar tumbuke wasu gurbatattun ma’aikatan gwamnati ba tare da yayatawa ba.

Daya daga cikin alkawarukan neman zaben Buhari a shekarar 2015 shine yaki da rashawa a kasarnan.

Shugaba Buhari ya tunatar da yadda ya samu nasara a yaki da da rashawa a lokacin da yake shugaban kasa na mulkin soja a farkon shekarun 1980.

Shugaban kasar ya bayyana damuwa dangane da yadda ake tafiyar da kananan hukumomi, inda yace a halin yanzu tamkar babu gwamnatocin kananan hukumomi a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: