Kungiyar Dattawan Kabilar Igbo, sun fitar da wata sanarwar kan matsalar rashin tsaro a yankin, inda suka bayyana cewa kimanin Matasa dubu 5,000 aka kashe tare da kama dubu 10,000 a yankin.

Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata Kasida da tsohon Gwamnan Jihar Anamba Chukwuemeka Ezeife; da tsohon Ministan Ilimi Farfesa Ihechukwu Madubuike; da Farfesa C.E. Nwekeaku; da Mista Onwu Arua Onwu da kuma Eze Ibe Nwosu suka sanyawa hannu.

Kungiyar ta fitar da sanarwar ne bayan wani taro da suka gudanar tare aikewa manema labarai a Abuja.

Matsalar tsaro da yankin yake fuskantar ne ya sanya hukumar yan sanda da rundunar Sojin Najeriya suka girke Ma’aikata a yankin domin zakulo Batagarin da suke kaiwa hare-haren a Ofishin Gwamnati.

Sufeta Janar na yan Sandan Najeriya ya zargi masu fafatukar Kafa Kasar Biafra da kaiwa hare-hare a yankin, zargin da suke karya tawa.

Kungiyar Dattawan Kabilar Igbo, sun koka kan cewa Jami’an tsaro sunyi sansani a yankin, tare da kafa shingaye da sunan neman yan Kungiyar IPOB, wanda hakan ya jefa fargaba a tsakanin Al’ummar yankin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: