Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ta fitar da mutane miliyan 10 da rabi daga kangin fatara da talauci.

0 53

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ta fitar da mutane miliyan 10 da rabi daga kangin fatara da talauci. Shugaban kasar ya fadi haka a yau a jawabinsa na ranar demokradiyya.

Ya lissafa manoma da kananan ‘yan kasuwa da masu aikin hannu da mata ‘yan kasuwa, daga cikin mutanen da rayuwarsu ta inganta a karkashin mulkinsa.

Shugaban kasar ya kuma ce gwamnatinsa tana bisa turba wajen cika alkawarinta na fitar da mutane miliyan 100 daga cikin kangin talauci.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zargi gwamnoni da jawowa kasarnan wahala sanadiyyar yajin aikin kungiyar ma’aikatan shari’ah ta kasa.

A lokacin da ya karbi bakuncin majalisar shiga tsakanin addinai ta kasa jiya a fadar shugaban kasa dake Abuja, shugaban kasar yayi magana dangane da jajircewarsa wajen mayar da ragamar mulki ga hannun jama’a.

Shugaban kasar ya kuma yi jawabi dangane da illar yajin aikin, inda ya jajanta matsalar da ya jawo kan harkokin tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: