Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya tana bukatar dala tiriliyan 1 da rabi

0 64

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya tana bukatar dala tiriliyan 1 da rabi cikin shekaru goma, domin cimma wani matakin da ya dace a fannin gine-gine da ababen more rayuwa.

Shugaban ya ba da wannan adadi ne jiya a birnin Glasgow na Scotland a wani babban taron inganta ababen more rayuwa na duniya wanda shugaba Joe Biden na Amurka da shugaban hukumar Tarayyar Turai Ursala Von Der Leyen da Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson suka shirya.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya ruwaito shugaban na cewa Najeriya a shirye take ta karbi masu saka hannun jari domin bunkasa ababen more rayuwa a kasar.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta dauki aikin fadada kayayyakin more rayuwa a Najeriya da muhimmanci, bisa la’akari da cewa sabbin masu saka hannun Jari a sassa masu muhimmanci na tattalin arziki zasu taimakawa wajen fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2030.

Shugaban kasa ya yi maraba da kasashen G7 kan shirin su na samar da biliyoyin daloli na zuba jarin samar da ababen more rayuwa ga kasashe masu karamin karfi da matsakaita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: