Shugaban mulkin sojan Gabon ya yi alkawarin mayar da kasar bisa tafarkin dimokuradiyya

0 294

Sabon shugaban mulkin sojan Gabon ya yi alkawarin mayar da kasar bisa tafarkin dimokuradiyya, amma ya ki bada lokacin da za a gudanar da sabon zabe.

Janar Brice Oligui Nguema ya ce hukumomin kasar zasu kara inganta tsarin dimokuradiyya kuma dakatar da su na wucin gadi ne kawai.

Sai dai gamayyar ‘yan adawar Gabon sun nuna shakku da abinda suka ce ba su ga alamun mika mulki ga gwamnatin farar hula ba.

An tsare tsohon shugaban kasar Ali Bongo a gidan kaso tun bayan tumbukeshi daga karagar mulki a wannan makon.

Da sanyin safiyar Laraba ne jami’an soji suka bayyana a gidan talabijin na kasar inda suka ce sun kwace iko, lamarin da ya kawo karshen mulkin shekaru 55 da iyalan Bongo suka kwashe suna mulki a kasar da ke tsakiyar Afirka.

Juyin mulkin da aka yi a Gabon shi ne na takwas a yammaci da tsakiyar Afirka tun shekarar 2020, bayan Nijar da Mali da Guinea da Burkina Faso da kuma Chadi.

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da tsohuwar shugabar mulkin mallaka Faransa da ke da alaka ta kut da kut da dangin Bongo sun yi Allah-wadai da matakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: