Sojoji Sun Ce Bello Turji Na Cikin Firgici Yayin Da Hare-Hare Ke Tsananta A Arewa maso Yamma

0 155

Rundunar sojin Najeriya ta ce jagoran ’yan bindiga Bello Turji na cikin firgici da rudani sakamakon tsauraran hare-haren soji a yankin Arewa maso Yamma.

Kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Warrah Idris, ne ya bayyana hakan yayin rangadin manema labarai a jihar Zamfara.

Sojoji sun ce bayanan sirri da fasahar leken asiri sun nuna Bello Turji na ta sauya maboyarsa akai-akai domin tserewa matsin lambar soji.

Rundunar ta karyata ikirarin cewa Bello Turji na iko da wata karamar hukuma, tana mai bayyana hakan a matsayin farfaganda ta ’yan bindiga.

Sojoji sun tabbatar da cewa Bello Turji da sauran shugabannin ’yan bindiga kamar Ado Aleru, Gwaska da Dogo Gide na fuskantar tsanantawar bin diddigi a dukkan yankuna.

Rundunar ta kuma karyata jita-jitar sakin ’yan bindiga 70, tana mai cewa babu wata sahihiyar sanarwa daga hukumomi kan hakan.

Leave a Reply