Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya bayyana cewa jiragen Air Nigeria da ake jira, zasu fara tashi nan da watan Afrilun shekara mai zuwa.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Hadi Sirika ya kuma bayyana cewa kamfanin jiragen saman zai kasance karkashin wani kamfani wanda gwamnati za ta mallaki kaso 5 cikin dari.

Ya kara da cewa, ‘yan kasuwan Najeriya za su rike kaso 46 cikin 100, yayin da sauran kaso 49 cikin 100 za a kebe su ga abokan huldar kasuwanci na nan gaba, ciki har da masu zuba jari na kasashen waje.

Ya kuma kara da cewa kamfanin idan ya fara aiki, zai samar da ayyukan yi kusan dubu 70 ga ‘yan Najeriya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: