Bankin Duniya ya fitar da rahoto da ke nuna cewa talauci a Najeriya zai karu da kashi 3.6 cikin dari nan da shekara ta 2027, musamman a kasashe masu arzikin albarkatu kamar Najeriya da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
A cewar rahoton *Africa’s Pulse* da aka fitar yayin taron bazara na Bankin Duniya da IMF a birnin Washington DC, ana hasashen cewa kasashen da ba su da albarkatu na ƙasa za su ci gaba da rage talauci fiye da waɗanda suka dogara da su.
Bankin ya ce hauhawar farashin kayan amfanin gona da kuma karancin tsadar man fetur na daga cikin dalilan da suka hana cigaba a kasashen da ke da albarkatu kamar Najeriya.
Har ila yau, rahoton ya jaddada cewa, gaggawar gyara harkokin rayuwa da samar da aiyuka na da matuƙar muhimmanci ga ƙasashe da ke da yawan jama’a da ke ƙaruwa cikin sauri, don hana talauci ci gaba da yawaita.