Taliban: An hana mata komawa makarantar sikandire a Afghanistan

0 108

An hana Mata Komawa Makarantar Sikandire a Afghanistan, bayan yan Taliban sun umarci Dalibai Maza da kuma Malaman su koma Makaranta domin cigaba da karatu.

A watan da ya gabata ne Kungiyar Taliban karbe ikon kasar ta Afghanistan, bayan ta kawar da gwamnatin shugaba Asharaf Ghani.

Sanarwar da Taliban ta fitar a jiya bata bawa Malamai Mata da Dalibai Mata damar komawa Makarantar ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwar ta kan halin da Mata a kasar suke ciki da kuma Makomarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: