An kama mutum 2 daga cikin wayanda suka kashe dangidan Sen. Bala Ibn-Na-Allah

0 94

2 daga cikin wadanda ake tuhumar su da kashe dan gidan babban dan siyasar nan Ibn na Allah mai suna Abdulkareem, wanda babba da ne ga Sen. Bala Ibn-Na-Allah, sunce sun sayar da motar marigayin ne akan Naira miliyan 1 a jihar Katsina.

Wadanda ake zargin masu suna Bashir Muhammad mai shekaru 23, da Nasiru Balarabe mai shekaru 27 sune suka bayyana hakan, a lokacin da suke amsa tambayoyi daga yan jaridu bayan jami’am  yan sandan jihar Kaduna sun samu nasarar cafke su.

A cewar jami’in yada labarai na rundunar yansandan jihar ASP Muhammad Jalige, ya gayawa manema labarai cewa darajar motar ta kai naira miliyan 9 amma suka sayar da ita akan Naira Miliyan 1.

Yayin amsa tambayoyi guda daga cikin wadanda ake zargin mai suna Balarabe wanda mazaunin kawo ne dake jihar Kaduna, yace bayan sun raba kudin yayi amfani da shi wajan sayo shinkafa yar waje amma hukumar hana fasakauri ta kasa Custom ta kama shinkafar.

Shi kuwa Muhammad cikin bayanansa, ya bayyana cewa kafin su kashe mutumin baima san wanene shi ba, inda ya kara da cewa ba talauci bane ya sanya shi a cikin wannan mummunan aikin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: