Timipre Sylva Ya Karbe Tikitin Takarar Gwamnan Jihar Bayelsa Na Jam’iyyar APC

0 79

An bayyana Timipre Sylva a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Bayelsa na jam’iyyar APC.
Shugaban kwamitin zaben, Manjo Janar AT Jibrin mai ritaya ne ya bayyana sakamakon zaben a sakatariyar jam’iyyar APC na jihar dake Yenagoa.
AT Jibrin ya ce Timipre Sylva ya samu kuri’u dubu 52 da 61 inda ya doke sauran ‘yan takara biyar.
Shugaban kwamitin ya godewa masu ruwa da tsaki a jihar bisa yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na gwamna cikin kwanciyar hankali.
A jawabinsa na karbar, Timipre Sylva, wanda tsohon minista ne, ya nemi goyon bayan sauran ‘yan takarar domin samun nasara ga jam’iyyar APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: