Ahmed Usman-Ododo Ya Zama Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar APC A Jihar Kogi.

0 92

Ahmed Usman-Ododo ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kogi.
A cewar Patrick Obahiagbon, sakataren kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na jihar Kogi, Usman-Ododo ya samu kuri’u dubu 78 da 704 inda ya doke sauran ‘yan takara shida.
Patrick Obahiagbon ya taya shugabannin jam’iyyar da mambobin jam’iyyar murnar gudanar da zaben fidda gwani cikin kwanciyar hankali.
Sakataren kwamatin ya kuma godewa Gwamna Yahaya Bello, bisa yadda ya tabbatar da tsarin dimokuradiyya.
A wani batun kuma, jam’iyyar PDP ta nada tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi a matsayin shugaban kwamitin zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kogi.
Sakataren jam’iyyar PDP na kasa Umar Bature ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.
Umar Bature ya shawarci ‘yan kwamitin da su nuna kyakkyawan hali ta hanyar bin dokoki da ka’idojin aikinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: