Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya koka kan rashin ababen more rayuwa na gwamnatin tarayya a wasu sassan jihar.

Kashim Shettima ya sanar da haka a jiya, lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin cibiyar lafiya na majalisar wakilai a Abuja.

Kwamitin ya shirya taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin kafa kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da kimiyar lafiya ta tarayya a garin Chibok da cibiyar lafiya ta tarayya a Gwoza.

A yayin da yake jawabin goyon bayan kudirin, Kashim Shettima ya ce kafa cibiyoyin biyu zai yi matukar tasiri ga al’ummomin biyu da suka fuskanci hare-haren mayakan Boko Haram.

Kashim Shettima, wanda a halin yanzu Sanata ne da ke wakiltar mazabar Borno ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC, ya koka da cewa mazabun biyu na tarayya ba su da wata cibiyar gwamnatin tarayya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: