‘Yan Najeriya 523 aka yi safararsu zuwa kasar Mali daga shekarar 2003 zuwa 2021 – NAPTIP

0 50

Hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP) tace ta ceto ‘yan Najeriya 523 da aka yi safararsu zuwa kasar Mali daga shekarar 2003 zuwa 2021.

Wani babban jami’in hukumar, Bori Ogunkanmi, ya sanar da haka a jiya yayin wani taron karawa juna sani da kungiyar cigaban tattalin arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta shirya a Abuja.

Taron na wuni uku zai mayar da hankali akan dakile safarar mutane, da hakkokin yara, da kare su, da sanya yara aikatau da kuma tsaron gaggawa wanda ya hada da ‘yan gudun hijira da kuma shirye-shiryen dokar jin kai ta kasa da kasa.

Yace hukumar NAPTIP ta kuma ceto mutane dubu 17 da 246 da aka yi safararsu tare da sauya musu rayuwa ta hanyar ilimintar da su karatun boko da ilimin sana’o’i domin dogaro da kai.

Yace hukumar daga kafa ta, ta shigar da daruruwan kararraki a gaban kotuna wanda ya jawo hukunta masu safarar mutane 500, yayin da wasu kararrakin ake cigaba da sauroronsu a kotunan, wasu kuma aka mika su zuwa hukumomin da suka dace domin cigaba da bincike domin yanke hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: