Tsohon Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ya kaddamar da wasu manyan ayyuka

0 82

Kwanturolan Hukumar Shige da Fice na Kasa Mai barin gado Muhammad Babandede, ya ce shekara 1 da Shugaban Kasa ya kara masa, ya bashi damar karasa wasu gine-gine, da ayyuka a hukumar, ciki harda Dakin Fasaha da sauran su.

A cewarsa, hakan yana daga cikin abubuwan da ya samarwa hukumar.

Babandede ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabin ban kwana, bayan ya karbi faretin girmamawa a Ofishin Hukumar dake Abuja.

Haka kuma ya ce samun karin shekara 1 ya bashi damar kammala wasu ayyukan a hukumar ta Immigration.

Mista Muhammad ya ce kawo yanzu kimanin ayyuka 14 yayi nasarar kammalawa wanda suka hada da Dabtarin kula da Iyakoki, da tsarin Visar Najeriya da sauran su.

Kwanturolan mai barin gado wanda shine shugaban hukumar 16, an nada shi ne a ranar 16 ga watan Mayu na shekarar 2016, kuma shine Kwamandan hukumar na farko da aka taba yiwa Faretin girmamawa na kammala wa’adinsa.

Cikin Mutanen da suka halarci taron sun hada da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, da Ministan Harkokin Cikin Gida Mista Rauf Aregbesola da kuma Ministan Sadarwa na Kasa Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami da sauran masu sarautun gargajiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: