Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci shugaban hukumar tara kudin shiga ta Jihar Alhaji Abdulrazak Salihi domin ya bayyana a gaban ta kan wasu aikace-aikacen hukumar.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Alhaji Labaran Madari wanda yake wakiltar Mazabar Warawa, shine ya kawo kudurin gayyatar shugaban hukumar cikin gaggawa a zaman da Majalisar da tayi a jiya.

Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Alhaji Abdullahi Yaryasa, shine na biyu, wanda ya fara goyan bayan kudurin.

Kakakin Majalisar Alhaji Hamisu Chidari shine ya sanar da gayyatar shugaban Majalisar, bayan Zauren ya amince da shugaban hukumar ta tara kudin shiga ya bayyana a gaban yau kenan14 ga watan Satumba.

Majalisar ta karbi wasikar Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na bukatar Majalisar ta tantance Mambobin hukumar kula da Ayyukan yan Majalisar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: