Tsohon ministan ma’aikatar kula da Harkokin Neja Delta a Najeriya Godsday Orubebe ya sanar da barin jam’iyyar adawa ta PDP.
Orubebe ya sanar da ficewar ne a wasikar da ya aike wa Shugaban jam’iyyar PDPn Iyorchia Ayu, in ji jaridar TheCable.
”Na zaci a lokacin da muka sha kaye a zaben shugaban kasa a 2015 a wani yanayi mai sarkakiya, jam’iyyar za ta yi amfani da lokacin da take da shi na zamanta babbar jam’iyyar adawa ta lalubo hanyoyin dawowa kan mulki”, in ji Orubebe.
A cewar Mr Orubebe halin da PDP take ciki a halin yanzu ya nuna cewa jam’iyyar ba ta shirya cin zaben 2023 ba.
Sunan tsohon ministan ya karade shafukan sada zumunta a lokacin zaben 2015, a lokacin da ya kasa ya tsare a zauren bayyana sakamakon zabe, yana ikirarin cewa INEC ba ta shirya yi wa PDP adalci ba.
-BBCHausa