

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Rundunar yan sanda a jihar Bauchi da ke Najeriya ta tabbatar da kai hari da kuma sace maigarin kauyen Zira, Alhaji Yahya Abubakar da dansa, Habibu Saleh a karamar hukumar Toro.
Mai magana da yawun rundunar SP Ahmed Wakil ne ya bayar da sanarwar ga manema labarai.
Ya ce yan bindigar sun auka kauyen ne da misalin karfe 12 na dare ranar Lahadi sannan suka yi awon-gaba da mutanen.
Ya kara da cewa yanzu haka jami’an tsaro sun bazu cikin daji don neman inda aka boye su.
“Muna bai wa al’umma tabbacin cewa za mu kwato wadanda aka sacen, in ji shi.
Sanarwar ta kuma nemi hadin kai daga al’ummar ta kuma neme su da su cigaba da lamuransu ba tare da damuwa ba.