Tsohon Sarkin Kano Sanusi na 2 ya ce biyan kudaden tallafin Man Fetur da gwamnatin tarayya take yi ‘‘Zamba ne’’

0 80

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 2, ya ce biyan kudaden tallafin Man Fetur da Gwamnatin tarayya take yi ‘‘Zamba ne’’ inda ya ce kusoshin gwamnati ne suke samun kudade a cikin sa.

Cikin watanni 7 da suka gabata kimanin Naira Biliyan 714 ne gwamnatin tarayya ta biya wajen biyan kudaden tallafin Man fetur a kasar nan.

Da yake tattaunawa da gidan Talabijin na Arise Tv, Sarki Sanusi ya ce gwamnatoci daban-daban sun cigaba da biyan tallafin man fetur din duk da cewa hakan yana yiwa tattalin arzikin kasa Illa baya ga ragewa gwamnati kudaden shiga.

Tsohon Sarkin Kanon wanda kuma tsohon gwamnan babban bankin Kasa ne ya ce halin da kasar nan take ciki a yanzu, yana daga cikin kura-kuran da gwamnatocin baya suka aikata.

A cewarsa, babu tunani yan Najeriya su rika sayan Mai da Araha a lokacin da yan Kasar suke bukatar ingantattun fannin Lafiya, da hanyoyin sufuri da Wutar Lantarki da kuma fasahar sadarwa.

Kazalika, ya ce gwamnatocin baya da mai ci yanzu, suna cigaba da biyan tallafin Man fetur ne saboda kusoshin gwamnati na samun Biliyoyin kudade da sunan tallafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: