Shugaba Buhari ya nanata kudurin sa na fitar da yan Najeriya Miliyan 100 daga cikin talauci

0 75

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nanata kudurin gwamnatinsa, na fitar da yan Najeriya Miliyan 100 daga cikin talauci nan da shekaru 10 masu zuwa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a sakon sa na taya yan Najeriya murnar cikar kasar nan shekaru 61 da samun yan cin kai wanda aka yada a kafofin yada Labarai jiya.

A cewarsa kudurin gwamnatin sa na fitar da yan Najeriya Miliyan 100 daga cikin kangin Talauci cikin shekaru 10 masu zuwa na nan akan hanya.

Haka kuma ya ce gwamnatin sa ta amince da daukar Matasa Miliyan daya aiki ta cikin shirin Npower daga dubu 500,000 da aka dauka a baya.

Shugaban Kasar ya ce Gwamnatin zata cigaba da aiwatar da shirin ciyar da Dalibai yan Makaranta a jihohi 35 da suke Najeriya cikin harda Abuja.

Kazalika, ya ce kimanin Mata dubu 103,000 ne aka dauka aikin dafa Abinci a kasar nan, inda kuma suke ciyar da Dalibai Miliyan 10 a kasa baki daya.

Shugaba Buhari, ya ce ya kuma umarci a cigaba da aiwatar da shirin bada bashi domin bunkasa tattalin arzikin kasar nan, kari akan Manoma Miliyan 1 da aka tallafawa ta cikin shirin Farmers Moni Program.

Leave a Reply

%d bloggers like this: