Gwamnan Ganduje ya ce abu mafi muni daga cikin Illolin yin kiwo a sarari shine yadda yayan Fulani basa zuwa makaranta

0 107

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce abu mafi muni daga cikin Illolin yin kiwo a sarari shine yadda yayan Fulani basa zuwa Makaranta.

Gwamna Ganduje ya fadi hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, inda ya ce matsalar kiwo a sarari ta haifar da abubuwa masu Illa da rudani.

A cewarsa, bai yarda da yadda Fulani suke tafiya a kafa ba, tun daga Arewa, zuwa Kudancin Kasar nan da nufin kiwo ba.

Haka kuma ya ce yin hakan baya bawa yayan Fulani damar zuwa Makaranta, wanda a cewarsa babban Laifi ne.

Dr Ganduje, ya ce Gwamnatinsa ta kirkiri wani shiri da ake kira Ruga System, a Dajin Dansoshiya, inda tsugunnar da Fulanin tare da samar musu da Ruwan sha, da Gidaje da Kasuwanni da Asibitocin Dabbobin su, da kuma Makarantu domin kulawa da karatun yayansu kamar kowanne dan Najeriya.

Kazalika, ya ce daga cikin Illolin yin kiwo a sarari shine yadda Yayan Fulanin da suke Kiwo basa samun Ilimi ingantacce.  

Leave a Reply

%d bloggers like this: