Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce bazata bar yancin samun kudaden Kananan Hukumomi ya shafi fannin Lafiyar ba

0 82

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce bazata bar yancin samun kudaden Kananan Hukumomi ya shafi fannin Lafiyar Jihar nan ba.

Mataimakin Gwamnan Jiha Malam Umar Namadi, shine ya bayyana hakan a taron tattaunawa kan Manufofin Jama’a a fannin Lafiya wanda Shirin bunkasa Ƙimar Dan Adam ya shirya a Cibiyar Horas da Ma’aikata da Manpower dake Dutse.

A cewarsa, kafin a fara aiwatar da shirin yancin kan Kananan Hukumomi Ma’aikatar Lafiya ta Jihar tana ware Naira Miliyan 10 duk wata, domin kulawa da Cibiyoyin Lafiya a matakin farko.

Malam Umar Namadi, ya ce fannin Lafiya na daya daga cikin shirye-shiryen da gwamnati take mayar da hankali.

Haka kuma ya ce wasu Kananan hukumomin suna fama da karancin Ma’aikatan Lafiya, saboda shirin sakarwa Kananan Hukumomi bara ta fannin kudade.

Kazalika, ya ce gwamnatinsu, zata yin duk mai yuwuwa domin bawa fannin Lafiya fifiko.

Leave a Reply

%d bloggers like this: