TUC da NLC Sun Umarci Ma’aikatan Abuja Su Koma Aiki, Bayan Taron Sulhu da Nyesom Wike

0 173

Kungiyoyin kwadago karkashin Trade Union Congress of Nigeria (TUC) da Nigeria Labour Congress (NLC) sun umarci mambobinsu da ke aiki a Babban Birnin Tarayya, Abuja, da su koma bakin aiki nan take, bayan wani taron sulhu da suka yi da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da tsakar dare.

Umarnin ya fito ne cikin wata takarda mai kwanan watan 3 ga Fabrairu, 2026, wadda aka aikawa dukkan kungiyoyin da ke karkashin TUC da NLC, tare da bayyana cewa an cimma matsaya bayan tattaunawa mai zurfi tsakanin bangarorin.

Takardar, wadda Sakatare Janar na TUC, Nuhu Toro, da Mukaddashin Sakatare Janar na NLC, Benson Upah, suka sanya wa hannu, ta bayyana cewa taron ya gudana ne bisa kiran Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan FCT, Sanata Mohammed Bomoi.

A cewar kungiyoyin, taron ya fara ne da karfe 11:45 na dare, inda ya kare da misalin karfe 3:51 na asuba, bayan abin da suka bayyana a matsayin tattaunawa mai tsawo, wadda aka ce an tattauna dukkan korafe-korafen ma’aikata tare da nemo musu mafita.

Kungiyoyin sun ce ministan ya ba su tabbacin girmamawa da ci gaba da tuntuba tsakaninsu da gwamnati, tare da amincewa cewa babu wani ma’aikaci da za a zalunta ko a dauki mataki a kansa sakamakon shiga yajin aikin da aka yi a baya.

Haka kuma, an cimma matsaya cewa dukkan shari’o’in da ke gaban Kotun Kwadago ta Kasa za a janye su nan take, lamarin da ya bai wa shugabannin kwadago damar umartar mambobinsu da su koma bakin aiki domin tabbatar da zaman lafiyar masana’antu.

Umarnin na zuwa ne bayan dakatar da zanga-zangar da aka shirya yi a Abuja, yayin da wakilan manema labarai suka lura da ma’aikata na komawa ofisoshinsu, a daidai lokacin da batutuwan shari’a da tsaro suka sanya gwamnati da ‘yan sanda gargadi kan duk wani yunkurin daukar matakin da zai iya kawo barazana ga zaman lafiya.

Leave a Reply