Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama wani da ake zargin fitaccen dan daba ne, mai suna Auwalu Ali, wanda aka fi sani da Auwalu Dan Daba, bisa zargin shirya hare-haren daba da tayar da tarzoma a cikin jihar.
Rundunar ta bayyana cewa an kama matashin mai shekaru 26 a ranar 31 ga watan Janairu, bayan jami’an ‘yan sanda na sashen Dorayi sun samu sahihan bayanan sirri kan ayyukansa.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Talata, a madadin Kwamishinan ‘yan sandan jihar.
A cewar rundunar, ana zargin Auwalu Ali da jagoranta gami da tsara kungiyoyin daba da ke kai hari tare da kwace dukiyoyin jama’a a wasu sassan birnin Kano.
A wani lamari mai nasaba da hakan, rundunar ta ce jami’anta daga sashen Sharada sun amsa kiran gaggawa a unguwar Sharada, inda aka kashe wani da ake zargin dan fashi ne bayan wasu mutane sun yi masa dukan tsiya.
Sanarwar ta ce harin ya jikkata wata mata matuka, inda aka garzaya da ita Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, kuma wani jami’in ‘yan sanda ya bayar da jininsa domin ceto rayuwarta.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya yaba da jajircewa da kwarewar jami’an, tare da gargadin jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, yana mai kira ga al’umma da su rika kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga hukumomi.