ukaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usuman Alkali Baba ya karbi ragamar jagorancin Rundunar daga hannun Mohammed Adamu mai barin gado.

Alkali ya karbi aiki shugabancin ne a Hedikwatar Rundunar, jim kadan bayan Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya daura masa sabon mukaminsa a ranar Laraba a Fadar Shugban Kasa.

Bikin mika ragamar shugabancin Rundunar ga Alkali yana gudana ne a dakin taro na Rundunar, inda manyan hafsoshin suka hallara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: