Hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, ta gano wasu gonaki uku da ake noma tabar wiwi a Jihar Kano.

Shugaban Hukumar reshen jihar, Isa Likita Muhammad ya ce sun kuma kama mutum biyar da ake zarginsu da noman tabar yayin da kuma suka samu nasarar gano wasu gidaje biyu da ake boye ta.

Sanarwar da Isa Likita ya fitar ta ce an gano gonakin ne a Kananan Hukumomin Gwarzo, Dambatta da kuma Ungogo da ke Jihar, inda aka samu tabar wadda nauyinta ya doshi tan daya.

Rahotannin da Hukumar NDLEA ta fitar a bayan nan sun nuna cewa Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da ake fama da matsalar shan kayan maye.

A tattaunawarsa da manema labarai na BBC Hausa, Isa Likita ya ce rashin wadatattun motocin fita aiki na daya daga cikin kalubalen da suke fuskanta wajen wayar kan al’umma a kan illar noman wiwi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: