Wani matashi mai shekaru 25 ya kashe matar dan’uwansa a Miga

0 165

Wani matashi mai shekaru 25 da ake kira da suna Danjuma Haruna anyi zargin cewa ya kashe matar dan,uwansa a kauyen Gamatan dake karamar hukumar Miga anan jihar Jigawa.

Kakakin rundunar yansandan jihar nan Lawan Shiisu Adam ne ya tabbatar da faruwar wannan lamarin a lokacin da yake tattauwa da manema labarai.

A cewarsa lamarin yafaru ne da yammacin ranar Talata, bayan matashin ya samu sabani tsakaninsa da matar dan’uwan nasa da ake kira da Zuwaira Bala a gidan ta dake kauyen Gamatan ta karamar hukuma Miga

Shiisu ya kara da cewa bayan sun samu sabani ne matashin yayi amfani da kafar sa wajan bugawa matar kafa a ciki, wanda yayi sanadiyyar suman ta a ranar 3 ga watan Agusta.

Haka kuma ya ce an dauki matar zuwa babban Asibitin Jahun, inda kuma a nan ne aka tabbatar da mutuwarta.

Kakakin rundunar ya ce bayan faruwar hakan ne mutumin ya tsere, sai dai yan sanda sun kamashi a nan Hadejia.

Kazalika, ya ce Kwamishinan yan sanda na jihar Jigawa Malam Usman Sule Gomna, ya umarci sashen Binciken Manyan Laifuka ya gudanar da bincike akansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: