Mutum 1 ya rasu a jiya biyo bayan wani hadarin Mota kirar Fijo 406 da wani Babur a kyauyen Gyara na Karamar hukumar Bogoro ta Jihar Bauchi.

Jami’in yada labarai na karamar hukumar Bogoro James Gomna, shine ya bayyana hakan, inda ya ce mutane 4 sun samu raunika a sanadiyar Hadarin.

A cewarsa, Hatsarin ya ritsa da wani Malami a Kwalegin Fasaha ta tarayya da ke Jihar Nasarawa Malam Nasiru B. Abdullahi da dan sa, Abdalla Nasiru da kuma daya Direban Namama Abdullahi.

Wanda suke cikin Motar sun samu raunika a sanadiyar Hadarin.     

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: