Labarai

Gidauniyar Khalifa Dankadai ta shirya wani jadawali domin horas da almajirai dubu 6,000 wanda suke karatu a tsangayun da suke Jihohi 6 na Arewa

Gidauniyar Khalifa Dankadai ta shirye wani Jadawali domin horas da Almajirai dubu 6,000 wanda suke karatu a tsangayun da suke Jihohi 6 na kasar nan.

Shugaban Gidauniyar Khalifa Dankadai, shine ya bayyana hakan a lokacin taron buda bakin watan Ramadan wanda ya shiryawa masu fafatika a shafikan sada zumunta na Kano.

A cewarsa, shirin zai farfado da Tsangayu da suke Jihohin Katsina, Kano, Niger, Jigawa, Zamfara da Sokoto.

Khalifa Dankadai ya ce za’a gabatar da shirin ne a Makarantun Tsangayu 60 da suke yankin Arewa, inda ya ce kowanne Jiha Almajirai dubu 1000 ne zasu amfana.

Haka kuma ya ce ya gayyaci mutane taron shan ruwan ne domin fadakar da su shirye-shiryen sa, tare da neman shawara ta yadda Gidauniyar zata kyautata tsarin.

Shima a Jawabinsa, Dan Majalisar tarayya mai wakiltar birni a Majalisar Kasa Hon Sha’aban Ibrahim Sharada, ya nanata kudurin Majalisar tarayya na farfado da makarantun Tsangayu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: