Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa tayi nasarar kama Katan 250 na Giya da sauran kayan maye a karshen makonnan.

Kwamandan Hukumar Harun Ibn Sina, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zagaya marasar wanda aka dauko a cikin wasu motoci 2, inda ya ce hukumar ta samu nasarar kama kayan ne bayan samun bayan sirri kan cewa motocin suna dauke da kayan maye wanda za’a kawo Kano.

Haka kuma ya ce hukumar tana cigaba da fadakar da al’umma kan illolin aikata manya-manyan laifukan.

Ustaz Harun Ibn Sina ya yabawa shugaban sashen yaki da shaye-shaye bisa yadda yake jajircewa wajen yaki da safara da shaye-shayen kwayoyi a Jihar.

Tun farko a jawabinsa, Shugaban Sashen yaki da shaye-shayen kwayoyi Malam Jamilu Yakasai, ya ce sun yi nasarar kama motoci 12 wanda suke dawo Barasa cikin watan Ramadan a Kano.

Haka kuma ya ce Barasar tana sashen ajiye kayan laifuka na hukumar da aka kama.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: