Wani sojan da aka kama da laifin tserewa daga bakin aikinsa tare da shiga cikin mayakan kungiyar Boko Haram don kai farmaki a wani gari ya kashe kansa

0 39

Wani sojan da aka kama da laifin tserewa daga bakin aikinsa tare da shiga cikin mayakan kungiyar Boko Haram don kai farmaki a wani gari, ya kashe kansa a lokacin da ake tafiya da shi.

Sojan mai suna Jibrin Biu da ke aiki da Bataliya ta 159 da ke Geidam ya bace ne tsawon kwanaki biyu kafin daga bisani a kama shi.

Wata majiya a rundunar soji ta bayyana cewa an gano sojan a cikin mayakan kungiyar Boko Haram ranar Lahadin da ta gabata, yayin da suka kai hari a garin Geidam a jihar Yobe.

A cewar majiyoyin, ciki har da abokan aikin sojan, an aike da sako zuwa sansanin sojojin da ke Gashua domin kama shi.

An kama shi ne a wani shingen bincike a cikin wata motar bas ta haya da ke tafiya zuwa jihar Yobe a safiyar ranar Talata.

Bayan kama shi, Ya kwace bindiga daga hannun wani sojan da ke tafiya da shi, inda ya harbe kansa har lahira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: