Wasu ƴan bindiga sun kashe sojoji 12 a wani artabu da suka yi a kudu maso yammacin ƙasar Nijar

0 147

Wani jami’in gwamnati a Jamhuriyar Nijar ya ce wasu ‘yan bindiga sun kashe sojoji 12 a wani artabu da aka yi a kudu maso yammacin ƙasar.

Jami’an tsaro sun fuskanci mummunan hari daga ɗaruruwan mayaƙa a kusa da kauyen Funio ranar Asabar.

Sai dai jam’in gwamnatin ya ce an kashe ‘yan ta’adda da dama.

Ana dora alhakin hare-hare na baya-bayan nan a yankin Sahel da ke yammacin Afrika kan mayaƙa masu alaka da kungiyar IS wadda ke iƙirarin jihadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: