Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da wata amarya da wasu mutum 5

0 97

Hakazalika, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Rigachikun dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da wata amarya da wasu mutane biyar.

Wata mata da aka sace wasu jikokinta ta ce amaryar mai suna Khadija tana kwance a gefenta lokacin da barayin suka shiga dakinsu.

Haka kuma a Jihar ta Kaduna, wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Sadiya, a jiya ta maka mahaifinta, Malam Usman, a gaban wata kotun shari’ar musulunchi da ke zamanta a Rigasa, Kaduna, bisa laifin yi mata auren dole.

Mai shigar da karar wacce ke zaune a Rigasa ta shaida wa kotun cewa wannan shine aurenta na uku ba da amincewarta ba.

Ta kuma shaidawa kotun cewa a halin yanzu tana zaune da wani mutum a Unguwan Sarki da ke Kaduna.

A nasa bangaren, mahaifin ya ce ‘yar ta sa ta kawo mutumin a matsayin wanda take so amma daga baya taki amincewa da shi.

Alkalin kotun, Malam Salisu Abubakar-Tureta ya umarci matar ta cigaba da zama a gidan Hakimin Rigasa sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Maris.

Leave a Reply

%d bloggers like this: