Labarai

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani ofishin ‘yan sanda a jihar Anambra, kasa da sa’o’i 24 bayan wani hari makamancin wannan a jihar

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani ofishin ‘yan sanda a jihar Anambra, kasa da sa’o’i 24 bayan wani hari makamancin wannan a jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce an kai harin ne a helkwatar ‘yan sanda ta Nteje da ke karamar hukumar Oyi a jihar a jiya da misalin karfe 3 na dare.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya, inda ya kara da cewa ‘yan sandan sun dakile harin, kuma sun samu nasarar kashe daya daga cikin ‘yan bindigar a lokacin da suke musayar wuta.

A wani batun kuma, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da ci gaba da gudanar da aikin rijistar masu kada kuri’a a wata karamar hukuma a jihar Imo sakamakon kisan da aka yi wa wani ma’aikacin hukumar.

Kakakin hukumar ta INEC, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a jiya, inda ya kara da cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe wani ma’aikacin hukumar a jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: