Asusun horas da ma’aikata na kasa ITF ya horas da matasa 100 a jihar Jigawa sanao’i’n girke-girke da tsara bukukuwa da koyan aikin ruwan famfo

0 68

Asusun horas da ma’aikata na kasa ITF ya horas da matasa 100 a jihar Jigawa sanao’i’n girke-girke da tsara bukukuwa da koyan aikin ruwan famfo.

Babban daraktan asusun, Joseph Ari, shine ya sanar da hakan a lokacin bikin rufe aikin bayar da horan a Dutse, Babban birnin jiha.

Yace matasan da aka zabo daga kananan hukumomin jiharnan 27 sun sami horan ne na tsawon watanni uku.

Joseph Ari wanda ya samu wakilcin Even Okiricha yace an horas da ‘yan Nigeria dubu 3 da 905 sana’o’in girke-girke da tsara bukukuwa, da koyan aikin ruwan famfo, tare da basu jari.

Ya roki gwamnatocin jihohi da kungiyoyi masu zaman kansu da yan siyasa da masu ruwa da tsaki dasu hada gwiwa da asusun a kokarin da yake na samarwa da al’umma sana’o’in dogaro da kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: