Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa ta amince da sayar da jiragen yaki da wasu na’urori ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Ana sa ran za a yi amfani da jiragen yakin a kan ‘yan ta’adda da sauran ‘yan bindiga da ke ta’addanci a kasarnan.

A cewar wata sanarwa da hukumar hadin kan tsaro ta Amurka ta fitar a jiya, na’urorin za su lakume kimanin dala miliyan 997 na gwamnatin tarayya, kwatankwacin sama da naira miliyan dubu 413.

Sanarwar ta ce kudaden da Najeriya za ta biya ya kuma shafi horar da ma’aikata wajen sarrafa kayan yakin.

Sayen jirgin da sauran na’urorin ya zo ne kasa da shekara guda bayan da gwamnatin Amurka ta baiwa kasarnan jiragen yaki samfurin Super Tucano guda 12, wadanda gwamnatin tarayya ta saya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: