Ya zuwa yanzu sama da mutane 340 ne aka tabbatar da mutuwarsu a lardin KwaZulu-Natal na kasar Afirka ta Kudu sanadiyyar ambaliyar ruwa a lardin mafi muni cikin shekaru da dama.

Firemiyan lardin, Sihle Zikalala, ya ce kimanin mutane dubu 41 ne lamarin ya shafa a kewayen birnin Durban.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe kwanaki ana tafkawa ya lalata gidaje da tituna da gadoji, lamarin da ya sa gwamnati ta ayyana dokar annoba a ranar Laraba.

An dawo da wutar lantarki da ruwan sha a wasu yankuna, amma hukumomi na yin kira da a yi hakuri saboda aiki ya yiwa kungiyoyin agaji yawa.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya dora alhakin matsalar kan sauyin yanayi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: