Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 18 a jamhuriyar Nijar

0 66

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 18 a jamhuriyar Nijar, a wani yanki da ke iyakar kasar da kasar Mali wanda aka dade ana samun afkuwar hare-haren da masu ikirarin kishin Islama ke kai wa.

Wani jami’i a yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa cewa wasu ‘yan bindiga a bisa babura ne su ka kai wa kauyen Deye Koukou hari da safiyar jiya Laraba.

An kai irin wannan harin ranar Lahadi a wani wuri da ke kusa da garin Banibangou, wanda mutame 14 su ka rasa rayukansu.

A watan Maris an kai wani hari a wannan gundumar ta kasar Nijar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 66.

A watan jiya ma hare-haren da aka kai a wata gundumar mai makwabtaka da wannan sun yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 19.

Leave a Reply

%d bloggers like this: