Labarai

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Shugaban kwamitin zaben Lawrence Ewhrudjakpo ne ya sanar da hakan a sakateriyar jam’iyyar PDP ta jihar, wajen da ake gudanar da zaben fidda gwani a Minna babban birnin jihar..

An ce an kashe wakilan ne a jiya yayin da suke komawa Mariga bayan da jam’iyyar ta dage zaben fidda gwanin sakamakon zanga-zangar da wasu ‘yan takarar suka yi da suka nuna rashin amincewa da jerin sunayen wakilan.

Daga nan aka bukaci wakilan da su kawo katin tantance sunayensu don tantance su.

An sauya wadanda suka rasa rayukansu a lamarin domin cika adadin wakilan karamar hukumar.

Sai dai, daya daga cikin wakilan, Shehu Haruna ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a tsakanin Mariga da Tegina kuma mutane hudu sun rasa rayukansu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: