Labarai

Dalilan da yasa wasu ‘yan takarar gwamna 2 na jam’iyyar APC suka yi watsi da zaman ganawar da gwamna Badaru ya kira domin a samar da dan takarar daya tal

Wasu ‘yan takarar gwamna biyu na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa, sun yi watsi da zaman ganawar da gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar ya kira domin a samar da dan takarar guda ta hanyar sulhu a jihar.

Ba a cimma matsaya a zaman ganawar ba.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya kira zaman ne a gidansa da ke Kano da nufin samar da dan takarar gwamna na bai daya.

Ba a ga ‘yan takara 3 cikin 9 masu neman takara a wajen zaman ba.

Bincike ya nuna cewa ‘yan takarar da ba su halarci zaman ba sun hada da tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Honorabul Faruk Adamu Aliyu da Alhaji Abba Muktari.

Zaman ganawar ya zo ne sa’o’i kadan gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a Kazaure.

Da aka tuntubi shugaban jam’iyyar APC na jihar Alhaji Aminu Sani Gumel ta wayar salula domin jin yadda zaman ya gudana, bai amsa kiran ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: