Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da ‘yan kasuwa bayan wani hari a hanyar Kaduna zuwa Abuja

0 37

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ‘yan kasuwa da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da suka kai wa ayarin motocinsu hari a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun yi fargabar kashe wani dan kasuwa daya, a lokacin da suka tare babbar hanyar da ke kusa dajin Unguwar Yako.

Manema labarai sun gano cewa wadanda abin ya shafa na kan hanyarsu ta zuwa jihohin Kaduna da Kano.

Wani mazaunin garin Buruku da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, sun kai wa ayarin motocin hari ne, inda yan bindigar suka yi awon gaba da wani adadi da ba a bayyana adadinsu ba, kuma an ce an kashe mutum daya daga cikin Mutanen dake kan hanyar Kano da Kaduna.

Wani ma’aikacin lafiya a Birnin Gwari shi ma ya tabbatar da harin inda ya ce daya daga cikin matan ma’aikatansu na cikin wadanda aka sace.

Kokarin tattaunawa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed, ya ci tura, domin har zuwa lokacin hada wannan rahoto, bai amsa kiran wayarsa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: