Yaƙin da ake a ƙasar Sudan zai iya yaɗuwa zuwa sauran ƙasashen Afirka – Abdel Fattah al-Burhan

0 228

Shugaban sojojin da ke mulki a Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya gargagi Majalisar Dinkin Duniya cewa yaƙin da ake gwabzawa a ƙasarsa zai iya yaɗuwa zuwa sauran ƙasashen Afirka, makwabta.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar jawabi a babban taron Majalisar da aka gudanar a birnin New York na ƙasar Amurka.

Janar Abdel Fattah ya kuma bukaci ƙasashen duniya sun ayyana abokin hamayyarsa, da ke jagorantar dakarun RSF a matsayin shugaban ƙungiyar ‘yan ta’adda.

Shugaban na Sudan yanzu haka na rangadin diflomasiyya, a ƙoƙarin neman goyon-bayan ƙasashen duniya bayan shafe watanni ana tafka yaƙin basasar da ya yi sanadin dubban rayuka.

Shi ma shugaban dakarun RSF, Mohamed Hamdan Dagalo ya aike da nasa saƙon bidiyo ga taron Majalisar, yana nuna a shirye yake ya tattauna tsagaita batun wuta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: