Sama da mutane 4,000 sun si rajista da shirin auren zawarawa a Kano

0 536

Hakumar Hisbah a jihar Kano sama da mutane dubu 4 ne suka yi regista da shirin auren zawarawa da gwamnatin jihar ta shirya yi wata mai kamawa.

Hisbah tace tayi nasarar tantance mutane dubu 1,800 da zata hada aure, kuma tuni ta tsara tantance duba lafiyar ma’auratan wanda ya zama wajibi gabanin shirye-shiryen shagulgulan bikin.

Da yake jawabi ga manema labari mataimakin babban kwamandan hakumar Mujahid Aminuddeen, ya bayyana cewa, wadanda aka tantance zasu halarci gwajin kwayar cutar HIV da kwayar halitta ta Genotype da gwajin kwayoyi gabanin daurin auren.

Mujahid yace gwamnatin jihar ta kuduri aniyar hada aurarraki 1,800 a rukunin farko, yayin da sama da mutane dubu 4000 suka yi regista.

Mallam Mujahid ya kara da cewa lura za matsin tattalin arziki da ake fama da shi a fadin kasa, mutane da dama suna fatab kasancewa cikin shirin musamman yammata da zawarawa wanda suka fito daga gidajen masu karamin karfi. Sai dai ya shawarci wadanda suka ci gajiyar shirin auren da su zauna, lafiya da aminci da juna, inda yayi gargadin cewa duk wadanda suka kashe aurensu ba tare da kwakkwaran dalili ba zasu biya gwamnatin jihar kudaden da ta kashe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: