Yadda aka kashe soja da wasu mutum biyar a wani hari da yan bindiga suka kai Jamhuriyar Benin

0 47

An kashe soja daya da ma’aikatan gandun daji biyar a wani hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a wani wajen shakatawa na kasa da ke arewacin Jamhuriyar Benin.

Akalla wasu mutane 10 sun jikkata a harin.

Harin kwanton bauna da aka yi a ranar Talata da yamma ya faru ne yayin wani aikin sintiri na yau da kullum a wani wajen shakatawa na kasa, wanda ya ratsa kan iyakokin jamhuriyar Benin, Burkina Faso da Nijar.

Dukkan kasashen uku dai suna shan fuskantar hare-hare daga mayakan da ke da alaka da al-Qaeda da kuma kungiyar IS.

An tura karin dakaru daga sojojin kasar Benin zuwa gandun dajin na kasa, wanda wata kungiyar agaji ta namun daji ta Afirka ta Kudu ke gudanarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: