‘Yan majalisar jihar Imo sun tsige kakakin majalisar Paul Emeziem a zaman da majalisar ta yi a yau.
‘Yan majalisa 19 ne suka tsige shugaban majalisar daga cikin ‘yan majalisar jihar 27.
A cikin takardar da aka karanta a zauren majalisar, ‘yan majalisar sun ce sun tsige Emeziem ne bisa zarge-zargen da suka hada da nuna rashin da’a da cin mutuncin ofishinsa da kuma babakere da kudaden jama’a.
‘Yan majalisar sun kuma zabi sabon kakakin majalisa Honarabul Kennedy Ibe.
A makon da ya gabata ne, Emeziem ya sanar da tsige makataimakin kakakin majalisar, Amarachi Iwanyanwu.
Bai kuma sanar da dalilin tsigewar ba.