Yadda akayi nasarar kubutar da kimanin mutane 48 daga safara a jihar Kano.

0 72

Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa ta bayyana cewa kimanin mutane 48 ne tayi nasarar kubutarwa a jihar Kano.

Kwamandan Hukumar na Shiyar Arewa Maso Yamma Malam Abdullahi Babale, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Jihar Kano.

A cewarsa, mutanen da hukumar ta kubutar basu wuce shekaru 11 zuwa 43 ba, wanda suka kunshi Maza 7 da Mata 41.

Kwamandan hukumar ya ce 14 are from Lagos State, Ondo 11, Kogi three, Akwa Ibom one, Rivers three, Oyo two, Osun one, Delta two and Ogun State 11.

Haka kuma ya ce hukumar ta samu bayanan sirri wajen gudanar da sumame domin kubutar da mutanen da ake kokarin ketarar da su zuwa Libya.

Jami’an hukumar da suke yin aiki a jihihon Kano da Katsina sune sukayi nasarar kubutar da mutanen.

Kazalika, ya ce suna cigaba da gudanar da bincike domin gano mutanen da suka dauki Nauyin tura mutanen zuwa Libya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: