Yadda bankado Ofishin Akanta-Janar na Tarayya ya cire biliyan N665.8 ba bisa ka’ida ba

0 124

Majalisar Dattawa ta bankado yadda Ofishin Akanta-Janar na Tarayya ya cire biliyan N665.8 ba bisa ka’ida ba daga Asusun Bunkasa Albarkatun Kasa da Kudaden Zaman Lafiya.

Binciken Majalisar ya kuma gano cewa Ofisishin Akanta-Janar din ya da ba da kudaden rance ga hukumomin gwamnati daban-daban sabanin manufar asusun a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2015.

Majalisar ta fasa kwan ne a rahoton da Kwamitinta kan Asusun Gwamnatin Tarayya bayan ya binciki kudaden da hukumomin Gwamnatin Tarayya suka kashe daga 2015-2018 bayan rahoton binciken da babban Odita-Janar na Tarayya ya fitar.

Game da rage Kudade na Musamman, rahoton na Odita-Janar ya ce, “Kimanin Naira biliyan 455.8 aka cire daga Asusun Bunkasa Albarkatun Kasa a matsayin rance ga mabukata daban-daban tsakanin 2004 da 2015, sabanin manufofin asusun na samar da kudade don bunkasa wasu albarkatun karkashin kasa banda mai da iskar gas.

Bayanan wadanda suka amfana da kudaden sun nuna an biya hakkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da Mataimakinsa, Namadi Sambo, wanda yawansu ya kai kimanin Naira biliyan daya da rabi, a ranar 11 ga Yuni, 2015.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta karbi kimanin Naira biliyan 20 daga Asusun Raya Albarkatun Kasa, sai kuma da Naira biliyan 17.9 da ta samu daga Brown Rice Levy.

Majalisar Dattawa, a cikin kudurin ta, ta umarci Ofishin Akanta-Janar na Tarayya da ya tabbatar da mayar da kudaden cikin kwana 60.

Leave a Reply

%d bloggers like this: