Yadda Boko Haram Ta Raba Kyautar Makudan Kudade A Geidam Ga Talakawa

0 129

Mayakan Boko Haram na raba wa al’ummar garin Geidam Naira dubu ashirin-ashirin da zummar jin ra’ayinsu.

Kwararru sun ce maharan sa suka shafe kwanaki suna cin karensu babu babbaka sun bullo da salon rabon kudaden ne domin jan ra’ayin mutane su shiga kungiyar ko tausaya mata.

“Boko Haram sun raba wa mutanen da ke Geidam N20,000 a matasyin kyautar Ramadan. Wasu iyalan sun karba da son ransu, wasu kuma tsoro ne ya sa suka karba… saboda kar a yi musu bulala ko a kashe su idan ba su karaba ba,” inji Abba, mazaunin Geidam.

Tun a ranar Juma’a Boko Haram ta kai hari Geidam, inda ta yi garkuwa da mutane, lamarin da ya da wahalar da sojoji wurin kwace ikon garin daga hannun.

Wata mata da a garin da ta ce ’yan Boko Haram din sun yi musu wa’azi ta bayyana cewa “Abun na da ban tsoro, saboda suna iya daukar yaranmu su zama mayakansu. Ya kamata gwamnati ta dauki mataki.”

Dakarun gwamnati sun yi nasarar shiga garin a ranar Litinin, amma har zuwa Laraba mayakan na cikin garin.

Wasu iyalan da suka samu fita daga garin sun koma da zama wurin ’yan uwa da abokan arziki a Damaturu, hedikwatar jihar da garuruwan Dapchi, Babban Gida, Gashua da sauransu.

Wani masanin harkar tsaro ya ce jan ra’ayin mutane na daga cikin dabarun bangaren Boko Haram na ISWAP sabanin ra’ayin Abubakar Shekau.

Asalin rahoton;

https://aminiya.dailytrust.com/yadda-boko-haram-ta-raba-wa-mutanen-geidam-kyautar-kudade

Leave a Reply

%d bloggers like this: